Mamallakin tashoshin rediyo da talabijin na MUHASA Alhaji Muhammad Babandede OFR, ya zama Shugaban Majalisar Zartarwar Kungiyar Masu Gidajen Rediyo Da Talabijin Masu Zaman Kansu Na Arewacin Najeriya.
Wannan zaɓe na ƙunshe a cikin wata takarda ta musamman da Shugaban Majalisar Amintattu na ƙungiyar Alhaji Dokta Ahmed Tijjani Ramalan ya sanya wa hannu.
Shugaban Majalisar Amintattun ƙungiyar ta NBMOA ya ce Alhaji Muhammad Babandede OFR zai riƙe wannan muƙami ne an tsawon watanni 6.
Inda ake sa ran a zamansa na shugabancin wannan ƙungiya zai gudanar da zaɓen cike guraben da ake da su.
- MUHASA Ta Ɗauki Nauyin Horar Da ‘Yan Kannywwood 12 Dabarun Aiki
- Hukumar NNPC Da Matsalar Makamashi A Najeriya
Dokta Ramalan ya ce suna sa ran gogewar Alhaji Muhammad Babandede zai taimakawa ƙungiyar zuwa tudun mun tsira.
Ya kuma bayyana cewa suna da yaƙinin Alhaji Babandede zai samarwa ƙungiyar ‘yanci da mutunci a idon duniya.
Takardar ta bayyana cewa Alhaji Muhammad Babandede OFR zai shiga ofishinsa a matsayin shugaban majalisar zartarwar ƙungiyar daga ranar 1 ga watan Disamba, 2024.