Ƙungiyar makiyaya ta Najeriya KACRAN ta ce za a iya kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ta addabi yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya cikin kwanaki 45, idan gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin yankunan suka ba da cikakken goyon baya ga wani shirin sulhu da ta gabatar.
Cikin wata sanarwar da da shugaban kungiyar na ƙasar, Mohammed Khalil Bello ya fitar ya ce shirin ƙungiyar ya tanadi makonni biyu na farko domin tuntuɓa da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, kafin a shafe wata guda ana aiwatar da matakan samar da zaman lafiya.
Ta ce akwai isassun shugabanni da masana harkokin tsaro daga Arewa da za su iya taka rawa wajen ganin an magance matsalar.
KACRAN ta kuma jaddada cewa zaman lafiyar Arewa na da muhimmanci ga tattalin arzikin Najeriya, ganin cewa yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na daga cikin cibiyoyin samar da abinci a ƙasar.
Ta ce rashin tsaro na ci gaba da yin barazana ga noma, kiwo da sauran harkokin tattalin arziki.
Ƙungiyar ta yi nuni da abin da ta kira nasarar amfani da tattaunawa wajen rage rikice-rikice a jihohin Kaduna da Katsina, tana mai kira ga sauran gwamnonin yankunan da su rungumi irin wannan hanya wajen warware matsalolin tsaro.
Sai dai ƙungiyar ta yi gargaɗi cewa kafa ƙungiyoyin sa-kai a kan tushen ƙabilanci ka iya ƙara rikita matsalar tsaro.
KACRAN ta kuma buƙaci gwamnati ta amince da shirin zaman lafiyar da ta gabatar, tare da ɗaukar matakai kan duk waɗanda suka ƙi bin duk wata yarjejeniyar sulhu da aka cimma.
