• Home  
  • Ana Zargin Wata Mata Da Kashe Dan Kishiyarta Da Guba A Kaduna
- Babban Labari - Labarai

Ana Zargin Wata Mata Da Kashe Dan Kishiyarta Da Guba A Kaduna

Daga: Safiyanu Haruna Kutama Rundunar ‘yan sandan a jihar Kaduna sun damke wata mata da ke kauyen Malari a yankin karamar hukumar Soba ta jihar, bisa zargin kisan wani jinjirin kishiyarta ɗan wata uku da haihuwa. Al’amarin ya auku ne a makon da ya gabata a gidan da matar ke zaune tare da kishiyar tata, […]

Daga: Safiyanu Haruna Kutama

Rundunar ‘yan sandan a jihar Kaduna sun damke wata mata da ke kauyen Malari a yankin karamar hukumar Soba ta jihar, bisa zargin kisan wani jinjirin kishiyarta ɗan wata uku da haihuwa.

Al’amarin ya auku ne a makon da ya gabata a gidan da matar ke zaune tare da kishiyar tata, yayin da uwar jinjirin ta shiga bandaki, ta bar yaron shi kadai a waje. Tana dawowa sai ta tarar da jaririn nata a hannun uwar gidan.

Kakakin ‘yansandan jihar DSP Mansir Hassan, ya shaida wa BBC lamarin ya faru ne a ranar 13 ga watan Mayu:

”Bayan ta amshi yaron sai ta ga kumfa na fitowa daga bakin yaron da kuma yanayin nau’inshi yana canzawa. Wannan ya sa aka garzaya da yaron asibiti, inda kafin a garzaya da shi ma asibitin Allah ya amshi rayuwarshi.

Mai magana da yawun ‘yansandan yya ce bayan sun samu wannan labari ne suka tura jami’ansu inda suka yi nasarar kama wannan mata Zaliha, wadda bayan bincike ta tabbatar musu da kanta cewa, ta ba wannan yaro maganin asid ya sha domin ta kashe shi saboda kishi.

DSP Hassan ya ce, ”Abin da ya tabbatar mana bayan bincike shi ne, akwai kanin shi mai gidan wanda ya sayo mata asid ɗin bayan ta gaya mishi cewa ita fa ba ta sha’awar ganin wannan yaron.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai