• Home  
  • ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin biyan sabon albashi
- Babban Labari

ASUU ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin biyan sabon albashi

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU, ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki huɗu ta fara biyan sabon tsarin albashi da aka amince da shi ga malaman jami’o’i a faɗin ƙasar. Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a wani taro da aka gudanar a […]

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU, ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki huɗu ta fara biyan sabon tsarin albashi da aka amince da shi ga malaman jami’o’i a faɗin ƙasar.

Shugaban ASUU, Christopher Piwuna, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake gabatar da jawabi a wani taro da aka gudanar a Jami’ar Sa’adu Zungur da ke Jihar Bauchi.

Ya ce ƙungiyar ta bai wa gwamnati wa’adin kwanaki huɗu daga ranar da ya yi jawabin domin ta fara aiwatar da biyan sabon tsarin albashin, wanda aka amince da shi bayan tattaunawa mai tsawo tsakanin ɓangarorin biyu.

A cewarsa, idan gwamnati ta gaza aiwatar da hakan cikin wa’adin da aka bayar, ƙungiyar za ta ɗauki mataki mai tsauri.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000