• Home  
  • Hakimai ku nisanci siyasa ku yi shugabanci cikin adalci — Sultan
- Babban Labari

Hakimai ku nisanci siyasa ku yi shugabanci cikin adalci — Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III , ya gargaɗi sababbin Hakimai da aka naɗa a Jihar Sakkwato da su nesanta kansu daga sha’anin siyasa, inda ya jaddada nauyin da ke kansu na kasancewa shugabanni ga kowa ba tare da duba banbancin ra’ayi ba. Da yake jawabi a ranar Alhamis a fadarsa da ke […]

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III , ya gargaɗi sababbin Hakimai da aka naɗa a Jihar Sakkwato da su nesanta kansu daga sha’anin siyasa, inda ya jaddada nauyin da ke kansu na kasancewa shugabanni ga kowa ba tare da duba banbancin ra’ayi ba.

Da yake jawabi a ranar Alhamis a fadarsa da ke Sakkwato yayin taron naɗin sarautar Hakimai 21 da kuma Magajin Garin Sakkwato, Sultan ya jaddada muhimmancin shugabanci na gari ba tare da ɓangaranci ba.

Haka zalika, ya buƙaci sarakunan gargajiyan da su ƙulla dangantaka ta lumana da talakawansu.

“Kada ku kalli kowa daga cikin talakawanku a matsayin maƙiya. Dole ne ku yi mu’amala da su cikin lumana, sannan ku haɗa kan danginku,” in ji shi.

Sarkin Musulmi ya tunatar da waɗanda aka naɗan cewa muƙaman nasu daga Allah ne, inda ya kira su da su yi aiki da gaskiya da kuma sanin cewa za a yi musu hisabi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai