• Home  
  • Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kashe Naira Tiriliyan 8.8 ba tare da an tanade su cikin kasafin kuɗi ba.
- Babban Labari

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kashe Naira Tiriliyan 8.8 ba tare da an tanade su cikin kasafin kuɗi ba.

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kashe Naira Tiriliyan 8.8 ba tare da an tanade su cikin kasafin kuɗi ba. Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC  Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kashe kusan naira tiriliyan 8.8 na kuɗaɗin gwamnati ba tare da an tanade su a […]

Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da kashe Naira Tiriliyan 8.8 ba tare da an tanade su cikin kasafin kuɗi ba.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC  Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kashe kusan naira tiriliyan 8.8 na kuɗaɗin gwamnati ba tare da an tanade su a cikin kasafin kuɗi ba.
Cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu ranar Asabar, Atiku ya ce wani rahoto na Asusun Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana waɗannan kuɗin da aka kashe ba tare da cikakken bayani ba.
Ya bayyana lamarin a matsayin rashin bin ƙa’idodin tafiyar da kuɗaɗen gwamnati, tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike.
Ya kuma yi zargin irin wannan salon kashe kuɗi ya samo asali tun lokacin da Tinubu yake Gwamnan Jihar Legas, yana mai cewa ana amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen ɗaukar nauyin harkokin siyasa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000