Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara tattaunawa da wani kamfanin bincike da raya tsirrai na Masar, EFC Plants, domin samar da haɗin gwiwa kan amfani da fasahar zamani ta tissue culture wajen noman dabino da dankalin Turawa (Irish) a jihar.
Gwamnan na Jigawa, Malam Umar Namadi ne ya jagoranci wata tawagar ƙwararru da masu zuba jari zuwa birnin Alƙahira na Masar, domin tattaunawa kan yadda za a yi amfani da fasahar zamani wajen bunƙasa harkar noma a jihar.
Gwamnatin ta ce haɗin gwiwar zai taimaka wajen samar da ingantattun tsirrai marasa cututtuka, ƙara yawan amfanin gona da kuma jawo hankalin masu zuba jari zuwa harkar noma.
A yayin ziyarar, Gwamna Namadi da tawagar sun duba cibiyoyin kamfanin na EFC Plants da ke gudanar da bincike da ayyukan tissue culture da biotechnology, ciki har da gidajen noman tsirrai masu sarrafa yanayi, dakunan adana tsirrai masu ƙarfin ɗaukar tsirrai miliyan shida da ɗakunan binciken cututtukan tsirrai.
Tawagar ta kuma samu bayanai kan yadda ake samar da tsirrai ta hanyar fasahar tissue culture, tun daga zaɓen tsiron uwa da bincikensa a ɗakin gwaje-gwaje, har zuwa samar da ƙananan tsirrai, haɓaka su a wurare na musamman da kuma shirya su domin dasawa da kasuwanci.
Gwamna Namadi ya ce manufar gwamnatin ba wai kawai sayen kayan shuka daga kamfanin ba ce, sai dai samar da cikakkiyar alaƙa da za ta kawo fasaha da zuba jari cikin jihar.
“Hadin gwiwar da muke shirin yi da EFC Plants zai wuce sayen kayan shuka. Muna neman cikakkiyar alaƙa da za ta samar da musayar fasaha, bunƙasa ƙwarewar ma’aikatanmu, gudanar da bincike tare, jawo zuba jari mai zaman kansa da kuma samar da tsirrai masu inganci a Jigawa,” in ji shi.
Ya ce amfani da fasahar tissue culture da biotechnology zai taimaka wajen magance matsalolin da manoma ke fuskanta wajen samun ingantattun kayan shuka, tare da ƙarfafa matsayin Jigawa wajen amfani da fasahar zamani a harkar noma.
Gwamnan ya ƙara da cewa fasahar za ta taimaka wajen samar wa manoma ingantattun tsirran dabino da dankali, ƙara yawan amfanin gona da rage dogaro da kayan shuka daga ƙasashen waje.

Idan aka cimma yarjejeniyar, haɗin gwiwar zai fara mayar da hankali kan dabino da dankalin Irish, tare da samar da damar musayar fasaha, horas da ƙwararru, gudanar da bincike tare da samar da ingantattun tsirrai marasa cututtuka a jihar.
Gwamnatin ta ce Jigawa na da muhimmiyar dama wajen bunƙasa noman dabino saboda yanayin ƙasarta, yawan filayen ban-ruwa da kuma kusancinta da manyan kasuwannin cikin gida.
Haka kuma, jihar na da damar bunƙasa noman dankalin Irish ta hanyar samar da ingantattun iri marasa cututtuka da amfani da sabbin dabarun noma.
A ƙarƙashin shirin, gwamnatin jihar za ta yi aiki tare da EFC Plants, hukumomin jihar da abin ya shafa, kamfanoni masu zaman kansu da sauran masu zuba jari.
Matakan farko sun haɗa da gudanar da cikakken binciken fasaha da na tattalin arziki, tantance wuraren da za a kafa aikin, shimfiɗa tsarin kasuwanci da kuma tattauna tsarin haɗin gwiwar da ya dace.
Daga cikin tawagar waɗanda suka yi rakiyar Gwamna Namadi zuwa Masar akwai Darakta-Janar na Cibiyar Bincike ta Jigawa, Dokta Suleiman Rufai Babura; Darakta-Janar na Hukumar Kawo Sauye-sauyen a fannin Noma ta Jigawa, Dokta Saifullahi Umar; da Babban Daraktan Kamfanin Natay Agro Limited, Dokta Abubakar Isa Bamai.
Gwamnatin Jigawa ta ce ziyarar na daga cikin shirinta na bunƙasa harkar noma ta hanyar haɗa kimiyya, fasaha da jarin masu zaman kansu, domin ƙara yawan amfanin gona, ƙarfafa samar da abinci, samar da ayyukan yi da kuma buɗe damar fitar da kayayyakin noma zuwa ƙasashen waje.
