Najeriya Da Ghana Sun Haɗa Gwiwa A Fannin Noma
Wani kamfanin Najeriya mai suna EGTA Investment Limited, ya ƙulla yarjejeniya da wani rukunin kamfanonin ƙasar Ghana da ake kira Jospong Group of Companies, da nufin haɓaka noma.
Wani kamfanin Najeriya mai suna EGTA Investment Limited, ya ƙulla yarjejeniya da wani rukunin kamfanonin ƙasar Ghana da ake kira Jospong Group of Companies, da nufin haɓaka noma.
An tabbatar da mutuwar mutane takwas a Rugange da ke ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu, a jihar Adamawa, sanadiyar kifewar kwale-kwale a ƙarshen makon nan, kuma wasu mutane 15 sun ɓace a ruwa ba a gan su ba.
Gwamnatin jihar Kano ta ce za a dawo da karɓar Haraji kullum a hannun matuƙa baburan adaidaita sahu a faɗin jihar domin samar da cigaba ta ɓangaren sufuri.
Kwamishinan yaɗa labarai na jahar Kano Baba Halilu Ɗantiye, ya tabbatar da cewa suna shirye-shiryen gina wuraren kwana a gidajen yaɗa labaran gwamnati domin a sawwaƙa wa masu aikin dare su samu wurin bacci.
Wani jirgin saman United Nigeria Airlines ya zame, ya saki hanyarsa ta sauka da kimanin mita 200 a babban filin jirgin saman Legas na Murtala Muhammad
Rundunar yan sandan jahar Kano ta haramta gudanar da hawan Kilisa, da na angwanci da kuma zaman majalisi har sai an nemi izini daga Fadar Sarkin Kano.
A wannan makon ne Jami’ar Bayero ta Kano ta yi bikin yaye daliban da suka kammala karatun koyon aikin likita su 316
Gwamnatin jihar Jigawa ta tabbatar da cewa ta yi nasarar yashe kogin Hadeja a tazarar da ta kai kilomita 60 tare da gina katangar kariya a tsawon kilomita 100 domin magance matsalar ambaliyar ruwa da ake samu a jihar.
Bayan Yusuf ya mayar da waɗannan kuɗaɗe ne kuma, gwamnan jihar Kano ya buƙaci ganawa da shi domin miƙa masa godiyarsa bisa gaskiyar da ya nuna tare da neman sauran matasa su yi koyi da shi.