Hawan Kilisa A Kano Yanzu Sai Da Izini

Rundunar yan sandan jahar Kano ta haramta gudanar da hawan Kilisa, da na angwanci da kuma zaman majalisi har sai an nemi izini daga Fadar Sarkin Kano.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da kakakin  rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu.

CP Gumel ya ce sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon yadda wasu matasa ke yunƙurin mayar da hannun agogo baya kan abinda ya shafi tsaro a jahar domin sun gano cewa a irin wuraren ake  aikata laifuka.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.