Home » Ba Don Ni Ba Da Abacha Ya Kashe Obasanjo — Gowon

Ba Don Ni Ba Da Abacha Ya Kashe Obasanjo — Gowon

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Tsohon Shugaban Najeriya, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana yadda ya haƙurƙurtar da marigayi Janar Sani Abacha a kan kada ya kashe takwaransa, Olusegun Obasanjo da aka yi zargi da kitsa juyin mulki a shekarar 1995.

Gowon ya bayyana hakan ne wani biki na maraba da gabatowar shagulgulan Kirsimeti wanda Gwamnatin Jihar Filato ta shirya.Gowon wanda shi ne babban baƙo na musamman a yayin taron da Obasanjo ya kasance babban baƙo, ya bayyana cewa, “na rubuta wa Abacha wasiƙa mai ɗauke da shawarar cewa Allah Ya ba shi mulki ne domin ya aikata alheri ba akasin haka ba.

“Mai ɗakina na aika cikin tsakiyar dare ta kai wa Abacha wasiƙar a Abuja. Na miƙa roƙon kada ya zartar da wannan hukuncin.

Tsaftar Muhalli: Ina Gudunmawar ku? 

“Ina farin ciki da cewa duk wannan ta zo wuce kuma hatta bayan fitowa da kurkuku Obasanjo ya zama Shugaban Najeriya a 1999. “Sai dai mu tuna cewa irin wannan na faruwa ne kaɗai da taimakon addu’a da riƙo da gaskiya,” a cewar Gowon.

A shekarar 1995 ce dai marigayi Janar Sani Abacha ya kama Obasanjo tare da tuhumarsa kan kitsa yi wa gwamnatinsa juyin mulki.Duk da cewa Obasanjo bai amsa laifin ba, amma Gwamnatin marigayi Abacha ta yanke masa hukuncin kisa.Sai dai bayan shafe shekaru uku yana zaman gidan ɗan Kande, Obasanjo ya shaƙi iskar ’yanci bayan rasuwar Janar Abacha a ranar 8 ga watan Yunin 1998.

 

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?