Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) ta yi kira ga ’yan Najeriya da su sake tabbatar da jajircewarsu wajen bin ka’idojin dimokuraɗiyya, zama nagartattun ’yan ƙasa, ƙarfafa haɗin kan ƙasa da kuma taka rawar gani a harkokin mulki.
Babban Daraktan Hukumar, Lanre Issa-Onilu, ne ya bayyana hakan cikin saƙon da ya fitar domin bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga Yuni.
Ya ce ranar 12 ga Yuni tana da matuƙar muhimmanci a tarihin Najeriya, domin tana nuna jarumtaka, jajircewa da sadaukarwar da ’yan Najeriya suka yi wajen neman daƙile mulkin kama-karya tare da tabbatar da dimokuraɗiyya da kare haƙƙoƙin jama’a.
Malam Issa-Onilu ya bayyana dimokuraɗiyya a matsayin tsarin mulki mafi dacewa wajen tabbatar da adalci, gaskiya da rikon amana, saboda tana bai wa jama’a damar zaɓar shugabanninsu cikin ’yanci, sa ido kan ayyukan gwamnati da kuma shiga cikin harkokin tafiyar da ƙasa.
Ya ƙara da cewa ranar ba wai kawai rana ce ta tunawa da jarumai maza da mata da suka sadaukar da rayuwarsu domin tabbatar da dimokuraɗiyya ba, har ila yau rana ce ta murnar juriyar al’ummar Najeriya da ke ci gaba da kare martabar dimokuraɗiyya duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
Babban Daraktan ya jaddada cewa dimokuraɗiyya ba ta taƙaitu ga gudanar da zaɓe kaɗai ba. A cewarsa, tana buƙatar ci gaba da sa hannun jama’a a harkokin ƙasa, mutunta doka, karɓar ra’ayoyin mabambanta, cika nauyin ɗan ƙasa da kuma yin aiki domin cigaban al’umma baki ɗaya.
Haka kuma, ya yi kira musamman ga matasa da su guji yaɗa labaran ƙarya, kalaman ƙiyayya da tashin hankali na siyasa, tare da nisantar duk wani abu da zai iya kawo cikas ga haɗin kan ƙasa da dorewar cibiyoyin dimokuraɗiyya.
Ya tabbatar da cewa Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen wayar da kai domin ƙarfafa al’adun dimokuraɗiyya, ilimantar da jama’a kan haƙƙoƙinsu da nauyinsu, da kuma inganta zama nagartattun ’yan ƙasa.
Har ila yau, ya yaba da gudummawar hukumomin gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, kafafen yaɗa labarai da sauran abokan hulɗa wajen bunƙasa dimokuraɗiyya, zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
A ƙarshe, Malam Issa-Onilu ya buƙaci dukkan ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan rana wajen sabunta imaninsu da goyon bayansu ga tafarkin dimokuraɗiyya, tare da haɗa hannu domin gina Najeriya mai cike da haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa.

