Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban jamiyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar bashi da sha’awar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a zabe mai zuwa.
Ganduje ya bayyana hakan ne bayan bayyanar wasu hotunan fastar Ganduje ɗin tare da Gwamnan Imo Hope Uzodinma a matsayin mataimakinsa.Wannan na zuwa ne jim kaɗan bayan wasu rahotanni da suke nuna cewa ana ƙoƙarin tsige ganduje daga kujerar shugabancin ƙasar, inda za’a bashi muƙamin jakada.
To sai dai mai magana da yawun sa, Edwin Olufa, ya bayyana cewa hotunan an ƙirƙire su ne don haddasa fitini.