Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Farfesa Abdullahi Saleh Usman (Pakistan) a matsayin sabon Shugaban Hukumar Alhazai ta Najeriya (NAHCON).
mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yammacin Litinin.
Ajuri Ngelale ya ce, Majalisar Dattawa za ta tabbatar da naɗin Farfesa Usman a matsayin sabon shugaban hukumar.
Wannan na zuwa ne bayan an cire Jalal Arabi a matsayin shugaban NAHCON da aka naɗa watan Oktoban 2023.
Arabi ya samu matsala a sgugabancinsa ne akan aikin Hajjin 2024, wanda gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin Naira biliyan 90.
Hukumar EFCC da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin arziƙin Ƙasa Ta’annati, ta kama Arabi da sakataren hukumar, Abdullahi Kontagora kan zargin almundahana.
EFCC ta ce an ƙwato kuɗi Riyal 314,098 na ƙasar Saudiyya daga hannun Jalal Arabi.