Shugabar gidan Rediyo da Talabijin na Muhasa Aishatu B.Sule wadda ta halarci taron a Abuja ce ta rubuto mana cewa an rantsar da sababbin shugabannin kungiyar Ma’aikatan Kafafen Yada Labarai wato SNB wadanda aka zaba a Abuja.
An rantsar da su ne a walimar cin abincin dare a Otel din NICON LUXURY da ke birnin Abuja, bikin ya samu halartar masu ruwa da tsaki a harkar Rediyo da Talabijin.
A jawabinsa na karbar ragamar Kungiyar, Professor Umar Alhaji Pate, yayi alkawarin bijiro da kyawawan ayyuka da za su ɗora kungiyar kan turbar ci gaba mai ɗorewa.
Ya bayyana cewa ya saba yin irin wannan kokari a jami’o’in Bayero da Maiduguri wanda ya janyo musu tallafi daga gidauniyar McArthur kuma jami’o’in sun yi amfani da su wajen samar da karin dakunan karatu da sauransu.
Ya yi Amfani da damar ya kuma gode wa yan kungiyar da suka zabe su sannan ya yaba wa wadanda suka farfado da kungiyar wadda shekaru sittin kenan da kafa ta.
Tun da farko a jawabinsa na rantsar da sababbin shugabannin, Shugaban gidan Talabijin na kasa, NTA, Kwamared Abdulhamid Dembos, ya bukace su da su samar da kyakkyawawar alkibla ga kungiya.
Ya kuma yi kira garesu da su yi aiki tare domin ci gaban kungiya.
A yayin taron an karrama mashahuran masu ruwa da tsaki a harkar Rediyo da Talabijin da kuma mutanen da suka hidimta wa al’umma.
Daga cikin wadanda aka karrama kuma aka ba su kyaututtuka, akwai Muhammad Ibrahim, Makaman Ringim Tsohon shugaban gidan Rediyo da Talabijin na Tarayya, da Tony Limi Ikenna, da kuma Sa’a Ibrahim tsohuwar shugabar kungiyar Shugabannin Kafafen Yada labarai ta Kasa kuma tsohuwar shugabar gidan Talabijin na Abubakar Rimi a Kano.
COV: AS