• Home  
  • Ba na tsoron duk wata barazana daga Gwamnatin Tarayya a yayin zaɓen Osun — Gwamna Adeleke
- Babban Labari

Ba na tsoron duk wata barazana daga Gwamnatin Tarayya a yayin zaɓen Osun — Gwamna Adeleke

Gwamnan Jihar Osun kuma ɗan takarar jam’iyyar Accord Party, Ademola Adeleke, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa ba ya tsoron ƙarfin Gwamnatin Tarayya ko goyon bayan da wasu gwamnoni ke ba wa jam’iyyar APC gabanin zaɓen gwamna na ranar 15 ga watan Agusta. Adeleke ya siffanta kansa a matsayin garnaƙaki kuma sarkin aiki wanda ke da […]

Gwamnan Jihar Osun kuma ɗan takarar jam’iyyar Accord Party, Ademola Adeleke, ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa ba ya tsoron ƙarfin Gwamnatin Tarayya ko goyon bayan da wasu gwamnoni ke ba wa jam’iyyar APC gabanin zaɓen gwamna na ranar 15 ga watan Agusta.

Adeleke ya siffanta kansa a matsayin garnaƙaki kuma sarkin aiki wanda ke da goyon bayan talakawa, inda ya jaddada cewa abokan hamayyarsa ba za su iya murƙushe muradin al’ummar jiharsa ba.

Kasancewar Adeleke a jam’iyyar Accord ya zo ne bayan ficewarsa daga jam’iyyar PDP saboda rikicin cikin gida da ya addabi shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.

Duk da sauya sheƙar tasa, rassan jam’iyyar PDP na jihar sun amince su mara masa baya domin ganin ya kai gaci a zaɓen na ranar Asabar.

 

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai