Home » Ba Ni da Masaniyar Murabus Ɗin Shugaban Hukumar Shige da Fice -Aregbesola

Ba Ni da Masaniyar Murabus Ɗin Shugaban Hukumar Shige da Fice -Aregbesola

by Anas Dansalma
0 comment

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, a jiya Laraba, ya musanta masaniya kan umarnin da aka bayar na yin murabus din mukaddashin Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Isah Idris Jere.

Yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a fadar shugaban kasa, a karshen taron majalisar zartarwa na tarayya na mako-mako wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar shugaban kasa a Abuja, Ministan ya ce, Ba shi da wata masaniya a kan haka.

A baya da,i kafafen yaɗa labarai sun rawaito cewa, Hukumar Kula da Shige da Fice ta kasa, ta mika wa mukaddashin kwanturola Janar na Hukumar, Isah Idris takardar sanarwar ritaya daga ranar 24 ga Afrilu, 2023 ko kuma kafin ranar.

A takardar an rubuta cewa, “Na rubuta ne domin in ja hankalinku game da cikar wa’adin shugabanci na shekara daya da Shugaban kasa ya ba ku ta takarda mai kwanan wata Afrilu 22, 2022, kuma wanda wannan wa’adi zai kare ranar 24 ga Afrilu, 2023.

“Saboda haka, an umurce ka da ka mika ragamar shugabancin ga babban mataimakin Kwanturola-Janar yanzu ko kuma kafin ranar Litinin, 24 ga Afrilu, 2023, har zuwa lokacin da Shugaban kasa zai nada babban Kwanturola-Janar na Hukumar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi