Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen da ya wuce a Najeriya, Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce ba zai yi wa gwamnan Kano mai jiran gado, Abba Kabir Yusuf, katsalandan cikin harkokin mulkinsa ba.
Kwankwaso, wanda shi ne jagoran NNPP na ƙasa, kuma wanda ake gani a matsayin ubangidan Abba Gida-Gida a siyasance, ya ce idan gwamnan mai jiran gado ya nemi shawararsa, zai ba shi.
Wasu mutane sun yi ta nuna fargabar cewa ba lallai ne Abba Kabir Yusuf ya samu cikakken ikon tafiyar da gwamnatin Kano ba, idan an rantsar da shi, saboda mai yiwuwa Kwankwaso zai yi ta ba shi umarni da yi masa katsalandan.
Sai dai, yaayin wata hira daMANEMA LABARAI, tsohon gwamnan na Kano, ya ce a matsayinsa na ɗan Kano zai riƙa ankarar da gwamnatin wadda za a rantsar a ƙarshen watan Mayu, duk lokacin da ya ga ta kauce hanya.
A cewar Kwankwaso, abin da yake so a sani shi ne ”ko wane ne yake mulkin Kano, ko soja ko ma wane ne, to ba za Su kyale shi, ya yi rashin kyautawa ba.”
Kwankwaso ya ce, shi abin da ya sani, shi ne za a gyara duk wasu abubuwa da aka yi ba daidai ba, a lokacin gwamnati mai barin gado.
Ya kuma ce, za su yi hakan ne don a gyara Kano ta yi kyau.