Babban Bankin kasa wato CBN ya ce tsoffin takardun Naira da aka sake wa fasali, za su ci gaba da zama halastattun kudi har bayan wa’adin farko da hukumomin kasar suka sanya na 31 ga watan Disamban 2023.
Ya ce an dauki matakin ne bisa dacewa da tsarin hada-hadar kudi na kasashen duniya da kuma hana sake maimaita abin da ya faru a baya.
Wata sanarwa da daraktan sadarwa na Babban Bankin, Isa AbdulMumin ya fitar, ta ce CBN na aiki da hukumomin da ke da ruwa da tsaki wajen ganin an soke hukuncin kotu da ya ba da umarni kan karewar wa’adin takardun kudin.