Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya ya bayyana takaici kan yadda ya ce ana samun ƙaruwar hare-haren da ake kai wa ‘yan sanda a sassan ƙasar.
Egbetokun Olukayode Adeolu, ya kuma yi kashedi da kakkausan harshe game da hakan.
Shugaban ƴan sandan ya bayar da umarni a gudanar da cikakken bincike kan irin waɗannan hare-hare, don a zaƙulo masu aikata su, kuma a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.
Har wa yau Rediyon Muhasa ta tuntubi Farfesa Ali Ado Siro, masanin dabi’un jama’a da binciken manyan laifuffuka, kuma Shugaban Sashen Nazarin Dabi’ar dan Adam da Harkokin Tsaro a Jami’ar Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa, domin jin abubuwan da suka haifar da karuwar hare-haren da ake kai wa yan sanda:
Ita ma rundunar ƴan sandan jihar Kano Rediyon Muhasa ya tuntubi kakakkinta SP Abdullahi Haruna Kiyawa domin mu ji ko suma ana kawo musu irin wadannan hare-hare, kuma me suke yi su kare kansu.
Dangane da ƙorafe-ƙorafen da ake yi na zargin cin zarafi da ƴan sanda ke yi wa jama’a kuma Babban Sufeton ƴan sandan Egbetokun Olukayode Adeolu, ya umarci dukkanin kwamishinonin rundunar a jihohi su buɗe wani sashe domin gabatar da irin wannan ƙorafi.
A bisa tanadin da hukumar ta yi na samar da sashen shigar da korafin cin zarafin jama’a da ake kira CRU (Complaint Response Unit), duk mutumin da yake da ƙorafi a kan ƴan sanda zai iya gabatar da shi ta hanyoyin sadarwa na zamani ba sai ya je ofishinsu ba, domin a bi masa hakkinsa.