Iyalan marigayi, Alhaji Nuhu Yashe, Bebejin Katsina, sun bayyana wasu daga cikin kyawawan halayensa na ɗaukar ɗawainiyar jama’a wajen kula da lafiya da ciyarwa da kuma cigaban rayuwarsu.
Wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da alhinin rashin, Alhaji Nuhu Yashe, Bebejin Katsina, wanda ya rasu ranar Alhamis da ta gabata.
Babban ɗan marigayin, mataimakin shugaban hukumar shigi da fici mai ritaya, Dikko Nuhu Yashe, ya bayyana cewa haƙiƙa an yi babban rashi, domin kuwa yanzu haka akwai ‘yan gudun hijirar da marigayin yake ciyarwa da kuma sauran al’ummar da yake ɗaukar ɗawainiyarsu.
Dikko Nuhu, ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da gidan Talabijin da Radio na Muhasa, a birnin Katsina ranar Juma’a.
- Babu Abinda Marigayi Bebejin Katsina Yafi So Kamar Ciyarwa – Dikko Nuhu Yashe.
- Gwamnonin Jahohin Ribas Da Osun Da Taraba Sun Kauracewa Taron PDP

Ya ce Bebejin Katsina, ya yi fice wajen ciyar da al’umma, har ya bayar da misalin almajirai kusan 150 ko ma fiye da haka, da suke zuwa gidansa cin abincin dare.
Ya kara da cewa da rana ma, akwai mutanen da ke zuwa karbar abinci, a ciki har da makotansa da ƴaƴansu.
Baya ga haka kuma akwai mutanen da ke zuwa daga kauyuka ya ɗauki nauyin su na zuwa asibiti, tun daga wajen kwana da abinci da kuma kudin maganinsu har su samu lafiya.
Dikko Nuhu ya ƙara da cewa akwai ma gidan da marigayin ya ware takanas don yan gudun hijira ta zauna a ciki, kuma shi ne ke ciyar da su, har yanzu suna nan a zaune a cikin gidan.
Dikko Nuhu Yashe, ya yi addu’ar Allah ya jikan mahaifin nasu ya gafarta masa da ma sauran al’ummar Musulmin duniya baki daya.
Marigayi Alhaji Nuhu Yashe, Bebejin Katsina, ya rasu yana da shekaru 96, ya bar mata 2, da ƴaƴa 21, kuma ana ci gaba da zaman makokin rashinsa a birnin Katsina.



