Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zaɓi Kabiru Tanimu Turaki (SAN) a matsayin sabon Shugabanta na ƙasa, a wani babban taro da jam’iyyar ta gudanar a birnin Ibadan na Jihar Oyo a juya Asabar.
Zaɓen na sa ya zo ne bayan wani rahoton da gidan talabijin na Channels ya fitar, inda ya tabbatar da cewa tsohon ministan harkoki na musamman ɗin ya samu rinjayen mambobin jam’iyyar, tare da amincewa daga manyan jiga-jigan PDP musamman daga shiyyar Arewa.
Tanimu Turaki, wanda ya kasance lauyan babban kotu (SAN), ya yi alkawarin gudanar da shugabanci na hadin kai da sauye-sauyen da za su farfado da jam’iyyar, yana mai jaddada cewa PDP za ta sake komawa matsayin karfin siyasar da ta yi kaurin suna a kai.
A jawabinsa bayan sanar da shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen, Turaki ya ce: “Lokaci ya yi da PDP za ta sake jan hankalin ‘yan Najeriya da manufofi na gaskiya da cigaba. Jam’iyyarmu za ta saurari jama’a, ta kuma yi aiki don dawo da amincewar al’umma.”
