• Home  
  • Bankin Duniya Ya Sanya Nera Cikin Jerin Kuɗaɗen Daba Su Da Daraja A Afrika.
- Babban Labari - Labarai

Bankin Duniya Ya Sanya Nera Cikin Jerin Kuɗaɗen Daba Su Da Daraja A Afrika.

A cikin wani rahoto da bankin duniyar ya fitar, Naira da ƙasar Najeriya ke amfani da ita na ɗaya daga cikin takardun kuɗi marasa daraja a Afirka ta yamma a shekarar 2024. Cikin wata ƙididdiga da ya fitar a yanzu Naira na daidai da kuɗin Birr na ƙasar Habasha da kuma Fan na ƙasar Sudan […]

A cikin wani rahoto da bankin duniyar ya fitar, Naira da ƙasar Najeriya ke amfani da ita na ɗaya daga cikin takardun kuɗi marasa daraja a Afirka ta yamma a shekarar 2024.

Cikin wata ƙididdiga da ya fitar a yanzu Naira na daidai da kuɗin Birr na ƙasar Habasha da kuma Fan na ƙasar Sudan a ɓangaren karyewa.

Rahoton ya ƙara da cewa buƙatar da ake samu na Dala a kasuwanni na daga cikin dalilin da ya sa Kuɗin ke karyewa .

A yanzu dai ana canza Dala ɗaya akan Naira 1700. Daga watan Agustan 2024, Naira ta faɗi da kusan kaso 43 cikin 100.

#bankinduniya #Najeriya #newmedia

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai