Tsohon mai tsawatarwa a majalisar dattijai kuma kusa a jam’iyyar APC Sanata Ali Ndume ya ce bazai daina gayawa gwamnatin tarayya gaskiya ba ko da zai rasa ransa.
Sanatan mai wakiltar Borno ta kudu ya nu na alhininsa kan yadda gwamnati ke kawo tsare-tsare da suke tsaurarra rayuwa ga al’ummar kasa.
Ndume ya ce ” Kowa ya san halin da ake ciki a kasar nan kuma kowa yana dandana kudar sa. Ba kuma laifi bane don an fadawa shugaba gaskiya.
To sai dai wannan kalamai na Ndume bai yi wa jam’iyyar APC dadi ba, wanda yasa ta fitar da sanarwar yi wa Sanatan gargadi.
Jam’iyyar ta kara da cewa Ali Ndume yana da muhimmanci a cikin jam’iyyar, bai kamata ya rika tozarta jam’iyyar a idon duniya ba.
A watan Yulin da ya gabata ne jam”iyyar ta aikewa majalisar dattijai wasika kan ta dakatar da Sanatan saboda su ka da yake yiwa gwamnatin. Daga bisani Sanatan ya nemi afuwa sai dai har yanzu ba’a mayar dashi kan mukaminsa ba.
Ndume ya yi korafin cewa ba ya samun damar ganin shugaban kasa shi yasa yake fada a bainar jama’a.
Na rubuta sau biyu, na yi ma wa’anda suke kusa da shi magana. Kuma maganan da na yi gaskiya ne, kundin mulkin ƙasa ya ba ni damar haka.”
A cewarsa, haƙƙi ne a kansa, ya ba da shawara a matsayinsa na dattijo.
APC dai ta ce babba mai ƙima kamar Ali Ndume, bai kamata a ce ana yamaɗiɗi da sunansa a matsayin wanda ke ƙoƙarin tozarta martabar jam’iyya ba.
Amma Ndume ya ce a duk bayanansa babu inda ya aibata wani, kuma babu inda ya soki jam’iyya ko shugaban ƙasa.
Ya ce duk maganar da ake yi matuƙar dai game da shawara ce, to yana nan a kan matsayinsa.
Sanatan ya ce ya bi duk hanyar da zai iya bi don ganin ya samu damar ganin shugaban ƙasar saboda ya bayyana masa halin da ƴan Najeriya ke ciki amma bai yi nasara ba.
- Maganar cewa ni babban ɗan jam’iyya ne wanda zan iya ganin shugaban ƙasa, ba haka ba ne.”
Ya ce yana magana ne domin sauke nauyin al’umma da ke kansa a matsayinsa na mai wakiltar jama’a.