Daga: Binta Abba Yakasai
Wasu bankunan kasuwanci a Najeriya sun fara aiwatar da sabon ƙarin kuɗin tura saƙon SMS daga Naira 4 zuwa Naira 6.
Wannan kari ya jawo ce-ce-ku-ce daga kwastomomi. Wannan sauyi ya fito ne cikin wasu saƙonni da bankunan suka aikewa kwastomominsu a safiyar Laraba.
A cewar bankunan, wannan ƙarin ya biyo bayan hauhawar farashin sadarwa da kamfanonin sadarwa suka aiwatar a baya-bayan nan.
- Gwamnonin Arewa Maso Gabashin Najeriya Na Ganawa Kan Tsaro A Yankin
- ACF Ta Sanya Sharadi Ga Masu Neman Goyon Bayan Arewa A Zaben 2027
Bankunan sun ce suna da bukatar daidaita da sabon tsarin farashi domin ci gaba da baiwa kwastomomi sabis na SMS kamar sanar da ma’amala da sauran bayanai.
Sai dai, zuwa yanzu Babban Bankin Najeriya, CBN, bai fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan ƙari ba.
Kwastomomi da dama na bayyana damuwarsu kan yadda ƙarin kuɗi ke kara yawa daga bankuna, duk kuwa da ƙalubalen tattalin arziki da suke fama da shi a halin yanzu.

