Daga : Shareep Khaleepha Sharifai
Rahotanni daga jihohin Arewa Maso Gabashin Najeiya na cewa gwamnonin yankin na taro a Damaturu babban birnin Jihar Yobe kan matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
Taron na zuwa a daidai lokacin da yankin ke fama da sabin hare-haren mayakan Boko Haram.
- ACF Ta Sanya Sharadi Ga Masu Neman Goyon Bayan Arewa A Zaben 2027
- Gobarar Daji Da Iska Mai Ƙarfi Sun Afkawa Isra’ila
Masana da al’ummar yankin na cewa dama ce gwamnonin suka samu domin tattauna yadda za a shawo kan matsalar tsaro da ke addabar yankin.
A ranar Talata ne dai ƙungiyar ISWAP ta ɗauki alhakin kai wani harin bam da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 26 a garin rann dake jihar Borno.

