• Home  
  • Barawo Ya Sace Motar Dake Cikin Ayarin Motocin Gidan Gwamnatin Kano
- Babban Labari - Labarai

Barawo Ya Sace Motar Dake Cikin Ayarin Motocin Gidan Gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar Kano, inda ya sace wata motar Toyota Hilux kuma ya fita da ita ba tare da samun cikas ba. Binciken DAILY NIGERIAN ya gano cewa barayin sun shiga gidan ne ta Kofa ta 4, inda suka suka shiga harabar gidan gwamnati, suka kuma fice da motar […]

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar Kano, inda ya sace wata motar Toyota Hilux kuma ya fita da ita ba tare da samun cikas ba.

Binciken DAILY NIGERIAN ya gano cewa barayin sun shiga gidan ne ta Kofa ta 4, inda suka suka shiga harabar gidan gwamnati, suka kuma fice da motar .

Majiyoyi daga cikin gidan gwamnatin sun bayyana cewa bayan faruwar lamarin, an duba bidiyon CCTV, wanda ya nuna barayin sun fice ne ta babban ƙofar shiga da fita ta gidan gwamnati ba tare da wani ya tare su ba.

Rahoton ya nuna cewa Motar da aka sace na daga cikin ayarin motocin da ke yi wa mataimakin gwamnan Kano rakiya.

An rawaito cewa direban motar, Shafiu Sharp-Sharp, an tsare shi na ɗan lokaci domin yi masa tambayoyi kan lamarin.

Majiyar ta ce: “Tuni an fara bincike. Ana ci gaba da tambayar direban yayin da Babban jami’in tsaron gidan gwamnatin wato CSO ke nazarin hotuna da bidiyon CCTV.”

Ta ƙara da cewa an riga an mika bayanan motar ga jami’an tsaro domin gano inda ta shiga da kuma kama wanda ya yi satar.

Duk kokarin  jin ta bakin mai magana da yawun Gwamna Abba Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa, hakan ya ci tura domin bai amsa kira ko saƙon da aka tura masa ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai