• Home  
  • Dan Majalissar Wakilai Sagir Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP
- Babban Labari - Labarai

Dan Majalissar Wakilai Sagir Ƙoƙi Ya Fice Daga Jam’iyyar NNPP

  Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Municipal, Hon. Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi, ya fice daga jam’iyyar NNPP saboda rikicin shugabanci da ke ƙara ta’azzara a cikin jam’iyyar. Ya bayyana hakan cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugabar jam’iyyar ta mazabarsa a Zaitawa ranar 11 ga Nuwamba, 2025, inda ya ce ya yanke wannan shawara […]

 

Ɗan Majalisar Wakilai daga Kano Municipal, Hon. Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi, ya fice daga jam’iyyar NNPP saboda rikicin shugabanci da ke ƙara ta’azzara a cikin jam’iyyar.

Ya bayyana hakan cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugabar jam’iyyar ta mazabarsa a Zaitawa ranar 11 ga Nuwamba, 2025, inda ya ce ya yanke wannan shawara bisa ’yancin da dokar ƙasa ta bashi wajen zaɓar shiga wata ƙungiya.

Ƙoƙi, ya bayyana a hukumance ficewarsa daga jam’iyyar NNPP daga ranar Talata, 11 ga Nuwamba, 2025, bisa ga damar da kundin tsarin mulkin Najeriya da na jam’iyyar suka ba shi.

Barawo Ya Sace Motar Dake Cikin Ayarin Motocin Gidan Gwamnatin Kano

A ƙarshe ya godewa jam’iyyar NNPP bisa damar da ta ba shi, yana mai cewa goyon baya da amana da ya samu abu ne mai muhimmanci a gare shi, Kawo yanzu, bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai