• Home  
  • Kotu Ta Umarci Kwamandan Sojoji Ya Kai Mata Sojan Da Ake Zargi Da Halaka Dan KAROTA
- Babban Labari - Labarai

Kotu Ta Umarci Kwamandan Sojoji Ya Kai Mata Sojan Da Ake Zargi Da Halaka Dan KAROTA

Babbar Kotun Jiha karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta ci gaba da sauraron shari’ar da aka gurfanar da wani jami’in Soji mai suna Lance Corporal Tunde Momudu, da Yakubu Abdussalam da Sagiru Yusuf Bichi bisa tuhumar hadin baki domin aikata laifi da kuma kisan kai, laifukan da suke musantawa. Ana zargin wadanda ake tuhuma […]

Babbar Kotun Jiha karkashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Mahmud, ta ci gaba da sauraron shari’ar da aka gurfanar da wani jami’in Soji mai suna Lance Corporal Tunde Momudu, da Yakubu Abdussalam da Sagiru Yusuf Bichi bisa tuhumar hadin baki domin aikata laifi da kuma kisan kai, laifukan da suke musantawa.

Ana zargin wadanda ake tuhuma da daukar marigayi Yahaya Idris Ismail yayin da yake bakin aikinsa na Karota.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya shiga motar da suke amfani da ita bayan sun dauko wasu kaya, inda ake zargin sun gudu da shi.

Daga nan ne kuma ake zargin Sojan ya yi amfani da wuka ya yanki marigayin, sannan suka jefar da shi a karkashin wata gada, abin da ya janyo mutuwarsa.

A zaman kotun na  ranar Talata , Lauyan gwamnati mai gabatar da kara, Barista Lamido Abba Soron Dinki, ya roki kotu ta ba da damar neman ɗaya daga cikin wadanda ake tuhuma, Sojan da bai bayyana ba, duk da cewa an gudanar da zaman kotun har sau huɗu.

Kotun ta amince da bukatar, inda ta umarci kwamandan sojoji na Bukavu Barracks da ya tabbatar da kawo Sojan gaban kotu a zama na gaba, an kuma sanya ranar 5 ga Disamban shekarar 2025 domin ci gaba da sauraron shari’ar.

 

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai