Home » Barcelona ta Zamo Zakara Bayan ta Ragargaza Real Madrid Awasan Karshe.

Barcelona ta Zamo Zakara Bayan ta Ragargaza Real Madrid Awasan Karshe.

by Suraj Na iya Kududdufawa
0 comment

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta zamo zakara a gasar nan ta Super Cup da aka kammala a kasar Saudiyya.

Ta zamo zakara ne bayan ta lashe babbar abokiyar hamayyar ta a duniyar kwallon kafa wato Real Madrid daci 5 da 2.

Real Madrid ce dai ta fara jefa kwallo ta hannun danwasa Kylian Mbappe kana daga bisan Lamin Yamal ya rama sai Lewandowski ya kara kwallo ta biyu sannan shima Raphinha ya kara kwallo ta uku, Barcelona suka kara kwallo ta 4 daf da tafiya hutun rabin lokaci.

Ana dawowa Raphinha ya kara kwallo ta 5 inda nasarar Barcelona ta tabbata, bayan an baiwa mai tsaron gidan Barcelona katin kora shine Real Madrid ta jefa kwallo ta 2 ta hannun danwasa Rodrygo.

Sakamakon wannan kofi da Barcelona ta lashe da gagarumar nasara akan Real Madrid yanzu haka ta kafa tarihin lashe kofin har sau 15.

A tarihi dai Real Madrid ta lashe Barcelona sau 105 inda itakuma Barcelona ta lashe Madrid sai 102.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?