A karshen makonnan mai zuwa za a fafata wasan karshe na gasar Spanish Super Cup tsakanin jiga-jigan kungiyoyin da suke hamayya da juna a duniyar kwallon kafa wato Barcelona da Real Madrid.
Wannan wasan hamayya ana yimasa lakabi da El clasico kuma wasa ne mai matukar kayatarwa a tsakanini su da zarar suna fafata wasa.
Barcelona dai ta samu damar zuwa wasan karshen ne bayan ta lashe kungiyar kwallon kafa ta Athletic Bilbao daci 2 da nema a ranar Laraba, inda ita kuma Real Madrid ta lallasa Mallorca daci 3 babu ko daya a ranar Alhamis.
Barcelona za ta buga wasan karshe karon farko a karkashin sabon mai horas da su wato Hansi Flick inda za suyi yunkurin lashe kofin karo na 15 a tarihi.
Shi kuwa Carlo Ancelotti mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid shi kadai ya lashewa kungiyar kofuna 15 kala daban-daban kama daga gasar nahiyar Turai da gasar Laliga da gasar zakarun nahiyoyi da sauransu, inda yanzu zai yi hankoran lashe na 16 a tarihi, kuma shine mai horas war da yafi kowa yawan lashe kofi a dukkanin masu horas war da suka horas da Real Madrid tun daga tarihin kafa kungiyar zuwa yanzu.
Tun bayan da aka koma kasar Saudiyya da fafata gasar Spanish Super Cup sau daya Barcelona ta lashe kofin inda ta lallasa Real Madrid daci 3 da 1 a wasan karshe inda ita kuma Madrid ta lashe gasar sau uku ciki harda wasan da ta ragargaza Barcelina daci 4 da nema.
A ranar Lahadi 12 ga watan Janairun sabuwar shekarar da ake ciki ta 2025 za a fafata wasan karshen tsakanin mashahuran kungiyoyin guda biyu, idan ba a manta ba a kakar wasa ta bana sun hadu a gasar Laliga inda Barcelona ta yiwa Madrid dukan kawo wuka daci 4 da nema.
Za a fafata wasan karshen a filin wasa na King Abdullah Sports City dake a birnin Jeddah na kasar ta Saudiyya, kuma alkalin wasa Gil Manzano ne zai jagoranci busa wasan.
An hango magoya bayan kungiyoyin a sassa daban-daban na duniya suna cika baki akan kowa yana ganin kungiyar da yake goyon baya ce zata lashe kofin.