• Home  
  • Buhari Jajirtaccen Abokin Aiki Ne Kuma Dattijon Kirki – Goodluck Jonathan
- Babban Labari - Labarai

Buhari Jajirtaccen Abokin Aiki Ne Kuma Dattijon Kirki – Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana marigayi tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a matsayin mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa ga aikinsa kuma ya yi wa ƙasar aiki yana cike da kishin ta.” Bayan samun labarin rasuwar mutumin da ya cire shi daga ofishin shugaban ƙasa a 2015, Mista Jonathan ya bayyana alhinin sa […]

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana marigayi tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a matsayin mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa ga aikinsa kuma ya yi wa ƙasar aiki yana cike da kishin ta.”

Bayan samun labarin rasuwar mutumin da ya cire shi daga ofishin shugaban ƙasa a 2015, Mista Jonathan ya bayyana alhinin sa inda ya ce Najeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin jigo a shugabanninta.

Goodluck Jonathan ya kasance shi ne shugaban ƙasa mai ci a jamiyyar PDP wanda kuma ke neman wa’adi na biyu, kafin Muhammadu Buhari na jamiyyar APC ya kayar da shi a zaɓen shugaban ƙasa.

” Na yi rashin abokin aiki mai mutumci kuma dattijon arziƙi. Tarihinsa zai ci gaba da kasancewa a zukatan mutanen da ke mutunta gaskiya da sadaukarwa da juriya da kuma jajircewa ga bin dokokin ƙasa,” in ji Jonathan.

Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba na musamman, mai kishin kasa, dattijo wanda ya yi wa kasa hidima a matsayin shugaban mulkin soji da shugaban farar hula dai-dai gwargwadon iyawarsa.

” Za a tuna shi a matsayin shugaba mai ƙarfin zuciya, soja mai kiyaye dokokin aiki, kuma ma’aikacin gwamnati mai jajircewa da ya yi ayyukan da za a yaba wajen samar da zaman lafiya da ci gaba ga ƙasar mu,” a cewar Jonathan.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai