Home » Buhari Ya Naɗa Sha’aban Sharada Sakataren Hukumar Kula da Almajirai Ta Ƙasa

Buhari Ya Naɗa Sha’aban Sharada Sakataren Hukumar Kula da Almajirai Ta Ƙasa

by Anas Dansalma
0 comment
Buhari Ya Naɗa Sha’aban Sharada Sakataren Hukumar Kula da Almajirai Ta Ƙasa

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya amince da nadin dan majalisar wakilai mai wakiltar karamar hukumar Kano Municipal mai barin gado, Honorabul (Dr) Sha’aban Sharada, a matsayin Babban Sakataren Zartarwar Hukumar kula da Almajirai da Yara Marasa zuwa Makaranta wanda kudirin kafa Hukumar ya samu sahalewa a 2023.

Sharada ya yi Digirinsa na farko a bangaren aikin aikin Jarida a Jami’ar Bayero ta Kano, sannan kuma ya yi Digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci daga Jami’ar Chichester da ke Birtaniya.

Sanarwar nadin ta fito daga Malam Garba Shehu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa a ranar Lahadi 28, ga Mayun 2023.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi