An Bada Hutun Maulidi A Najeriya
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 16 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar, domin bikin ranar Maulidin Annabi Muhammad S.A.W.
Gwamnatin Najeriya ta ayyana ranar Litinin 16 ga watan Satumba, a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan ƙasar, domin bikin ranar Maulidin Annabi Muhammad S.A.W.
Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci da Rashawa a Najeriya ta ce Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) sun kai samame ofishin su da ke Abuja.
Aƙalla mutum 45 ne suka ƙone ƙurmus a wani mummunan haɗarin mota da ya faru a kan titin Agaie-Bida dake Jihar Naija. Hatsarin ya haɗa da wata babbar motar dakon man fetur. Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a kusa da ƙauyen Man-woro da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Lahadi. Wani mazaunin […]
Shugabancin ƙungiyar Ƙwadago na ƙasa ƙarƙashin jagorancin Kwamared Joe Ajearo, tayi kira da gwamnatin tarayya da ta gaggauta soke ƙarin kuɗin fetur da tayi, inda suka bayyana cewa wannan abu ne mai matuƙar bayar da tsoro. Duba da har yanzu ba’a fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 70 ba. Shugaban Ƙungiyar NLC […]
Taron ACF Ƙungiyar Tuntuɓa Ta Arewacin Najeriya ya haɗa kan dattawan yankin a ɗakin taron dake hedikwatar ƙungiyyar a Kaduna
NNPCL ya tabbatar da ƙara kuɗin litar man fetur a Najeriya.
Sakamakon mamakon ruwan sama da ake ci gaba da tafkawa a sassa daban-daban na duniya, a yankin kasar Nijar an yi wani gagarumin ruwan sama a jihar Maradi inda yayi asarar rayuka da dama.
Hukumar zaɓe ta jihar Kano, KANSIEC, ta matso da zaɓen ƙananan hukumomi 44 da a baya ta tsara yi ranar 30 ga watan Nuwamba, 2024, zuwa ranar 26, ga watan Oktoba, 2024.
Wani matashi mai aikin shara a filin jirgin Malam Aminu da ke Kano ya mayar da Dala Dubu 10 da ya tsinta, kudin da sun kai kimanin Naira miliyan 16, da ya tsinta.
Babban Daraktan Hukumar ta NIA ya ce ba wani babban dalili bane ya sa shi ajjiye aikinsa.