Wani Jami’in Sojan Ƙasar Nan Ya Harbe Abokan Aikinsa Har Lahira
Rundunar sojin kasar ta tabbatar da shari’ar wani soja da ya harbe abokan aikinsa da kansa har lahira a sansanin Rabah, a Jihar Sokoto a ranar Lahadin data gabata .
Rundunar sojin kasar ta tabbatar da shari’ar wani soja da ya harbe abokan aikinsa da kansa har lahira a sansanin Rabah, a Jihar Sokoto a ranar Lahadin data gabata .
Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta cire sunan Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, daga jerin wadanda suka lashe zaben da aka gudanar a makon jiya.
Babbar katun daukaka kara ta kasar nan, ta bai wa dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da na jam’iyyar labour party peter obi izinin su binciki kayan da a ka yi amfani da su wajen gudanar da babban zaben shekarar 2023.
Ɗan takarar gwamnan na jam’iyyar Labour Party a jihar Adamawa, Umar Mustapha Otumba ya sanar da janyewa ‘yar takarar gwamna, kuma mace tilo a ƙasar nan sanata Aisha Ahmad Binani tare alƙawarin mara mata baya.
Kungiyar kiristocin ta Ƙasa, CAN, reshen Arewacin kasar nan ta bukaci duk mabiyanta da su kwantar da hankalinsu biyo bayan ayyana Bola Ahamad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar nan da Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta yi.
Ya yin da ya rage kasa da mako daya a gudanar da zaben gwamnoni da na yan’majalisar dokokin jihohi a kasar nan, Jami’an tsaro sun ce, sun gano wasu shirye-shiryen da manyan jam’iyyu masu adawa da juna ke yi domin tayar da fitina a lokacin zaben a wasu Jihohi.