NCC Ta Musanta Zargin Yayata Muryar Tarho Ta Peter Obi
Hukumar da ke sa ido kan kamfanonin sadawar ta Najeriya, NCC, ta nesanta kanta daga zargin da wasu ke yi cewa tana da hannu wajen kwarmata sautin muryar da aka ji ta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP Peter Obi da Bishop David Oyedepo suna tattaunawa.