• Home  
  • DSP Hussaini Abdullahi Ya Zama Sabon Mai Magana Da Yawun Rundunar Yan Sandan Shiya Ta Daya Zone One Kano.
- Babban Labari - Labarai

DSP Hussaini Abdullahi Ya Zama Sabon Mai Magana Da Yawun Rundunar Yan Sandan Shiya Ta Daya Zone One Kano.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da naɗe-naɗen sabbin masu magana da yawun rundunar wasu shiyyoyi, ciki har da naɗin DSP Hussaini Abdullahi a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar yan sandan shiya ta daya wato Zone 1, Kano. DSP Hussaini Abdullahi, wanda ya maye gurbin CSP Bashir Muhammad, ya kasance mataimakin kakakin rundunar […]

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da naɗe-naɗen sabbin masu magana da yawun rundunar wasu shiyyoyi, ciki har da naɗin DSP Hussaini Abdullahi a matsayin sabon mai magana da yawun rundunar yan sandan shiya ta daya wato Zone 1, Kano.

DSP Hussaini Abdullahi, wanda ya maye gurbin CSP Bashir Muhammad, ya kasance mataimakin kakakin rundunar yan sandan Jihar Kano, kafin wannan naɗin.

Rahotanni na cewa kwarewarsa da jajircewarsa wajen hulɗa da jama’a ne suka tabbatar da cancantarsa ga sabon matsayin da ya samu.

A cewar takardar naɗin, rundunar ta kuma nada wasu sabbin jami’an hulɗa da jama’a a wasu shiyyoyi na ƙasar, domin ƙarfafa sadarwa da inganta isar da sahihan bayanai, da tabbatar da cewa al’umma suna samun cikakkun rahotanni kan aiyukan tsaro a yankunansu.

Rundunar ta bayyana cewa waɗannan nade-nade na cikin tsarin sabunta shugabanci da ƙarfafa aikin hulɗa da jama’a a matakai dabam-daban.

Al’umma da dama sun taya sabbin kakakin murna tare da fatan Allah ya ba su nasara a sabbin ayyukan da aka dora mu su.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai