• Home  
  • El-Rufai ya sake gurfana a kotun Kaduna
- Babban Labari

El-Rufai ya sake gurfana a kotun Kaduna

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata kan tuhumomin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar a kansa. An gurfanar da El-rufai ne kan laifuka da suka hada da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, damfara, da bai wa […]

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya sake gurfana a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna a ranar Talata kan tuhumomin da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta shigar a kansa.

An gurfanar da El-rufai ne kan laifuka da suka hada da amfani da mukami ba bisa ka’ida ba, damfara, da bai wa wasu dama fiye da yadda ya dace, da kuma wasu tuhumomi da suka shafi kudade.

El-Rufai ya bayyana a kotun ne bayan ICPC ta sake shi daga tsare shin da tayi na fiye wata guda, wanda hakan ya biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Ummar El-Rufai, a Cairo, Masar..

Bayan kammala gurfanan sa a Babbar Kotun Jihar, za a kai El-Rufai Kotun Tarayya da ke Kaduna, inda za a fara sauraron buƙatar belinsa da ya shigar.

Ana sa ran cewa za a duba batun belinsa cikin gaggawa, saboda irin nauyin tuhumomin da ake masa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai