Hukumomi sun bayyana cewa tankar, wadda ke ɗauke da fiye da lita 36,000 na man fetur, ta fashe ne bayan da burki ya ƙwacewa matukinta a kan tudun Mutengene Hill, inda ta riƙa gangarowa.
Karfin fashewar ya haddasa tashin gobara da ta laƙume wani banki da ke kusa da inda lamarin ya faru, abinda ya tilasta wa mazauna yankin gudu domin tsira.
Rahotanni sun ce gidaje kusan 10 da kuma motoci da dama sun kama da wuta, yayin da gobarar ta ci gaba da ruruwa na tsawon lokaci.
Daga cikin waɗanda suka mutu akwai maza, mata da aƙalla yaro guda, inda da yawa daga cikinsu suka ƙone matuka har ba a iya gane su.
Okwandum Samuel Ndenzen, jami’in taƙaita faruwar ibtila’i na Red Cross a Limbe, ya bayyana cewa an gano waɗanda aka iya gani, amma ya ce ba a tabbatar ko adadin waɗanda suka mutu ya tsaya a nan ba, saboda har yanzu motoci suna wurin, amma zuwa yanzu an bincika ko’ina ba tare da gano ƙarin gawarwaki ba.
Bayanai sun ce an kai mutane uku da suka jikkata sosai zuwa asibitin Bingo, yayin da wasu sojoji da suka samu raunuka masu sauƙi aka yi musu magani a wurin.
Tsananin lamarin ya sa birnin Douala ya tura ƙarin jami’an kashe gobara, sannan aka samar da wata hanya ta wucin gadi domin sauƙaƙa zirga-zirga da ta tsaya cik.
Bayan hayaƙi ya lafa, garin Likomba ya fara tantance asarar da ibtila’in ya haifar, yayin da rahotanni suka nuna cewa ruwan kusa da wurin ya gurbace da man fetur, abin da ke tayar da fargabar yiwuwar barazanar lafiya ga al’ummar yankin.

