Jawabin Kim, wanda kafar yaɗa labaran gwamnati KCNA ta wallafa, ya nuna yadda aka ɗora wa sojojin ayyuka masu hatsari, musamman a yankunan da ake ci gaba da fuskantar barazanar fashewar bama-baman da aka binne tun bayan tashin rikice-rikice tsakanin Rasha da Ukraine.
Rahotanni daga hukumomin leƙen asiri na Koriya ta Kudu da ƙasashen Yamma sun nuna cewa Koriya ta Arewa ta tura dubban sojoji domin tallafa wa Rasha a yaƙin da take yi da Ukraine, wanda yanzu ya kusa cika shekaru huɗu da fara shi.
Masana harkokin tsaro na bayyana cewa a madadin wannan tallafi, Rasha na bai wa Koriya ta Arewa taimakon kuɗi, fasahar soja, da kayayyakin abinci da makamashi, matakan da ke taimaka wa Pyongyang wajen kauce wa tsauraran takunkumin ƙasa da ƙasa da aka kakaba mata kan shirye-shiryen makaman nukiliya da makamai masu linzami.
Wannan furuci na Kim na ƙara nuna zurfafa alaƙar soja da siyasa tsakanin Koriya ta Arewa da Rasha, a daidai lokacin da yaƙin Ukraine ke ci gaba da sauya yanayin tsaro da hulɗar ƙasa da ƙasa, musamman a nahiyar turai.
