Fitaccen Marubucin Najeriya, Farfesa Wole Soyinka, ya yi Allah wadai da kalaman Sanata Datti Baba Ahmed, ‘dan takarar mataimakin shugaban kasar karkashin Jam’iyyar Labour a zaben da ya gabata a kasar.
Soyinka ya bayyana irin kalaman da Baba Ahmed ke yi a matsayin karan-tsaye ga bangaren shari’a da kuma tafarkin dimokradiyar Najeriya baki daya.
Wannan ya biyo bayan kalaman ‘dan takarar yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels.
Ya bukaci shugaban kasar, Muhammadu Buhari, da alkalin alkalan Najeriya cewar kada su kuskura su rantsar da Bola Ahmed Tinubu, a matsayin zababben shugaban kasa.
Baba Ahmed ya bayyana cewar bayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi da kuma gabatar masa da takardar shaida da hukumar INEC ta yi ya saba wa dokar kasa.
Tuni Hukumar kula da kafofin yada labarai ta NBC ta ci tarar tashar Channels naira miliyan 5 saboda saba ka’idar aiki wajen bai wa Baba Ahmed, damar yin irin wadannan kalamai kai tsaye.