Hukumar da ke sa ido kan kamfanonin sadawar ta Najeriya, NCC, ta nesanta kanta daga zargin da wasu ke yi cewa tana da hannu wajen kwarmata sautin muryar da aka ji ta dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP Peter Obi da Bishop David Oyedepo suna tattaunawa.
Cikin tattaunawar ta wayar tarho, an ji Obi yana neman Bishop Oyedepo da ya taimaka masa wajen samun kuri’un Kiristocin yankin tsakiyar arewacin Najeriya, inda ya kwatanta lamarin da yaki na addini.
Yayin da magoya bayan Obi suke ikirarin hada sautin aka yi don a bata masa suna, wasu na cewa da ma Obi mutum ne mai nuna banbancin addini.
Sai dai yayin da wasu ke zargin hukumar NCC da yaɗa sautin, cikin wata sanarwa da NCC ta fitar dauke da sa hannun Darektan Yada labarai, Reuben Muoka, hukumar ta musanta taka wata rawa a fitar da sautin.
Muoka ya ce kamar yadda dokar sadarwa ta Najeriya ta shekrara 2003 da sauran dokokin kasa suka tanada, hukumar ba ta da ikon ta bi diddigin wata tattaunawar wayar tarho.
Kakakin hukumar NCCn ya kara da cewa, hukumar ta kai rahoton wannan zargi da ake mata ga jami’an tsaro domin su gudanar da bincike su kuma dauki mataki idan ya zama dole.
Bola Ahmed Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya zo na biyu, sai dan takarar jam’iyyar LP Obi da ya zo na uku.
Manyan jam’iyyu siyasar da suka hada da PDP da LP sun shigar da kara a kotu suna kalubalantar sakamakon zaben.