Wani rahoto da Hukumar ƙididdiga ta ƙasar Argentina ta fitar na nuni da cewa rabin mutanen ƙasar na fama da matsanancin Talauci.
Wannan na bayyana cewa an sami ƙaruwar talauci da kaso 40% cikin 100% na shekarar da ta gabata, kuma ya nuna tasirin matakan tsuke bakin aljihu da gwamnatin shugaban Ƙasar Javier Millei ta ɓullo da su.
Tun bayan hawan Mista Javier a watan Disambar 2023, Gwamnati ta rage tallafin da ta ke bayarwa kan man fetur da sufuri da makamashi da sauransu.
- UNICEF Ta Buƙaci A Samar da Shirye-shiryen Bunƙasa Rayuwar Yara
- HISBAH Ta Gano Masu Ɗaukar Nauyin Yaɗa Bidiyon Tsiraici
Hauhawar farashin kayayyaki a Argentina a cikin watan Agusta ya kasance ɗaya daga cikin mafi girma a duniya.