• Home  
  • HISBAH Ta Gano Masu Ɗaukar Nauyin Yaɗa Bidiyon Tsiraici
- Babban Labari - Labarai

HISBAH Ta Gano Masu Ɗaukar Nauyin Yaɗa Bidiyon Tsiraici

Hukumar HISBAH ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa sun gano waɗan da suke ɗaukar nauyin yaɗa biyon tsiraici da ke tashe a ‘yan kwanakin nan, Shugaban Hukumar a Jihar  Kano, Mallam Aminu Ibrahim Daurawa  ne ya bayyana hakan , inda yace a binciken da suka gudanar, sun gano cewa daga ƙasashen waje ake ɗaukar […]

Hukumar HISBAH ta Jihar Kano ta tabbatar da cewa sun gano waɗan da suke ɗaukar nauyin yaɗa biyon tsiraici da ke tashe a ‘yan kwanakin nan,

Shugaban Hukumar a Jihar  Kano, Mallam Aminu Ibrahim Daurawa  ne ya bayyana hakan , inda yace a binciken da suka gudanar, sun gano cewa daga ƙasashen waje ake ɗaukar nauyin masu yin waɗannan bidiyo kuma su yaɗa shi a kafafen sada zumunta.

A satin da ya gabata ta ne dai ake zargin wata budurwa da sakin faifan bidiyon ta tsirara  har na tsawon mintuna uku, babu ko zani a jikin ta.

Bayyanar wannan bidiyo ya haifar da cece-kuce a tasakanin mabiya shafukan na sada zumunta.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai