Hukumar kula da gidajen yari ta kasa ta bayyana cewa yanzu haka ta fara gudanar da bincike kan wasu fursunoni bakwai da suka tsere daga gidan yarin Ilesa dake jihar Osun.
Hukumar ta ce daurarrun sun tsere ne sakamakon ruwan sama mai karfi da ya lalata wani bangare na gidan yarin.
mai magana da yawun hukumar Umar Abubkar , ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar talata.
- Ma’aikatan KEDCO Za Su Tsunduma Yajin Aiki
- Yan Sandan Kano Sun Cafke Yan Fashi 6 Da Kwato Motocin Sata 4
A cewarsa, ruwan sama mai karfi ya karya bangon da ke kewaye da gidan yarin, wanda hakan ya ba wa fursunoni damar tserewa.
Shugaban hukumar kula da gidajen yari na kasa, Sylvester Ndidi Nwakuche, ya bayar da umarnin gudanar da bincike cikin gaggawa kan faruwar lamarin, tare da hada kai da hukumomin tsaro domin kamo fursunonin da suka tsere.