Ma’aikatan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO) za su shiga yajin aiki daga daren Talata wayewar garin Laraba, bisa zargin gazawar kamfanin wajen biyan kudaden fansho na ma’aikata.
Kungiyar Ma’aikatan Lantarki ta Kasa (NUEE) reshen shiyyar Kano — wadda ta kunshi jihohin Kano, Jigawa da Katsina — ce ta sanar da hakan a daren Talata.
Babban Sakataren Tsare-Tsaren kungiyar, Comrade Muhammad Babangida Muhammad, ya shaida wa manema labarai .
- Yan Sandan Kano Sun Cafke Yan Fashi 6 Da Kwato Motocin Sata 4
- Ba Don Mu Yi Rigima Da Bangaren Zartarwa Aka Zabe Mu Ba: Godswill Akpabio
Ya ce sun dauki matakin ne bayan dogon jinkiri da suka ce KEDCO ta yi wajen biyan hakkokin fanshon ma’aikatan da suka yi ritaya.
“Mun gaji da jira da kuma alkawuran da ba a cika ba. Don haka yajin aikin nan ba zai tsaya ba sai an biya bukatun ma’aikata,” in ji shi.
Yanzu haka, ana sa ran yajin aikin zai shafi samar da wutar lantarki a wasu sassan jihohin da KEDCO ke kula da su.