• Home  
  • Fursunoni 9 sun haddace Alƙur’ani a gidan yari a Kano 
- Babban Labari

Fursunoni 9 sun haddace Alƙur’ani a gidan yari a Kano 

Fursunoni tara da ke zaman kaso a Gidan Gyaran Hali na Tsaka-tsaki da ke Wudil a Jihar Kano sun samu nasarar kammala haddar Alƙur’ani Mai Tsarki. Wannan gagarumar nasara ta zo daidai da bikin cika shekaru 50 da kafuwar gidan gyaran halin. Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali tA Najeriya […]

Fursunoni tara da ke zaman kaso a Gidan Gyaran Hali na Tsaka-tsaki da ke Wudil a Jihar Kano sun samu nasarar kammala haddar Alƙur’ani Mai Tsarki.

Wannan gagarumar nasara ta zo daidai da bikin cika shekaru 50 da kafuwar gidan gyaran halin.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali tA Najeriya reshen Jihar Kano, CSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa, ya bayyana cewa wasu daga cikin fursunonin ba su da cikakken ilimin karatun Alƙur’ani lokacin da aka kawo su gidan.

A cewarsa, ta hanyar jajircewa, ladabi da kuma ingantaccen tsari na koyarwa a gidan yarin, fursunonin sun samu nasarar haddace Alƙur’ani baki ɗaya. Kofar Nassarawa ya bayyana cewa hakan ya  nuna tasirin shirye-shiryen gyaran hali na addini a cibiyar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000