Ganduje ya dawo Nigeria, yayin da Gwamnan Kano Abba ke shirin komawa APC

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya dawo Najeriya bayan shafe makonni yana hutun aiki a birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Kano , Muhammad Garba ya sanyawa hannu.

Ya ce Dr. Ganduje ya sauka a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Lagos a ranar Asabar da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, a cikin jirgin Emirates, kafin daga bisani ya wuce Abuja da ƙarfe 8 na dare.

Bayan dawowarsa, ana sa ran tsohon shugaban APC na ƙasa zai fara tarurruka da masu ruwa da tsaki, domin tattaunawa kan sabbin sauye-sauyen da ake samu a siyasa a jihar Kano.

Malam Muhammad Garba, yace an shirya waɗannan tattaunawa ne domin duba yadda yanayin siyasar Kano ke sauyawa, tare da yin shawarwari da shugabannin jam’iyya da sauran manyan masu ruwa da tsaki.

Haka kuma, ana sa ran Dakta Ganduje zai halarci aikin rajistar mambobin jam’iyyar APC ta hanyar na’ura (e-registration) da ke gudana a faɗin ƙasar nan.

Shirin rajistar, wanda Ganduje ya ƙaddamar a lokacin da yake Shugaban APC na ƙasa, an kirkiro shi ne domin sabunta rijistar mambobin jam’iyyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *