Gobara ta tashi a Kasuwar Singa da ke birnin Kano a safiyar Litinin ɗin nan.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan kasuwa da mazauna sun shiga tashin hankali matuƙa sakamakon tashin gobarar a shahararriyar kasuwar kayan abincin kwali da da ke titin Bello Road.
An yi asarar dukiyoyi na maƙudan kuɗaɗe a sanadiyyar gobarar ta safiyar Litinin, yayin da ake ci gaba da aiki ceto.

