• Home  
  • Gobara ta yi ajalin ɗalibai 16 a Kenya
- Babban Labari

Gobara ta yi ajalin ɗalibai 16 a Kenya

Ɗalibai 16 sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a makarantar kwana da ke Gilgil a Kenya, kamar yadda wani ɗansanda ya shaida wa manema labarai. Wasu ɗalibai 74 kuma suna samun kulawa a asibiti bayan raunin da suka ji. Gobarar da ta faru a makarantar ƴanmata ta Utumishi ta soma ne da sanyin […]

Ɗalibai 16 sun mutu sakamakon wata gobara da ta tashi a makarantar kwana da ke Gilgil a Kenya, kamar yadda wani ɗansanda ya shaida wa manema labarai.

Wasu ɗalibai 74 kuma suna samun kulawa a asibiti bayan raunin da suka ji.

Gobarar da ta faru a makarantar ƴanmata ta Utumishi ta soma ne da sanyin safiyar yau Alhamis lokacin da ɗaliban suke barci, in ji ƙungiyar agaji ta Red Cross a Kenya da kuma ƴansanda.

Ƴansanda sun ce ana aikin ceto sai dai zuwa yanzu hukumomi ba su gano musabbabin gobarar ba.

Ƙungiyar Red Cross a Kenya ta ce masu bayar da agajin gaggawa na wajen domin ba da tasu gudunmawar.

A yayin da yake magana da iyayen ɗalibai da sauran mutanen da suka taru a wajen makarantar, babban jami’in ƴansanda Masoud Mwinyi ya ce lamarin abin tashin hankali ne.

Dama a kan samu tashin gobara a makarantun kwana a Kenya inda a shekarun baya-bayan nan lamari ya janyo mutuwar mutane.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai