• Home  
  • Ko Ganduje ba zai ce shi ba yarona ba ne — Martanin Kwankwaso ga Abba
- Babban Labari

Ko Ganduje ba zai ce shi ba yarona ba ne — Martanin Kwankwaso ga Abba

Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya kuma jigo a jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya mayar wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, martani kan kalaman da suka shafi dangantakarsu ta siyasa. Idan ba a manta ba Gwamna Abba, ya soki kalaman Kwankwaso kan kiransa da ya yi da “yarona” duk da cewar da shekaru kaɗan ya girme […]

Jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya kuma jigo a jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya mayar wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, martani kan kalaman da suka shafi dangantakarsu ta siyasa.

Idan ba a manta ba Gwamna Abba, ya soki kalaman Kwankwaso kan kiransa da ya yi da “yarona” duk da cewar da shekaru kaɗan ya girme shi.
Sai dai yayin da yake magana da magoya bayansa a gidansa da ke Miller Road a Kano a ranar Laraba, Kwankwaso ya ƙaryata wannan magana.
Ya ce ko tsohon Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya taɓa zama mataimakinsa, ba zai iya musanta cewa ya taɓa kasancewa “yaronsa na siyasa” ba.

Kwankwaso, ya tambayi dalilin da ya sa wasu ’yan siyasa ke ƙin amincewa da rawar da suka taɓa takawa a ƙarƙashinsa a siyasa.

A wata hira da ya yi da Trust TV, Kwankwaso, ya kuma bayyana Gwamnan a matsayin “Abba PA,” inda ya jadadda cewa shi ne ya taimaka masa har ya kai matsayin gwamna daga ƙaramin matsayi a siyasa.

Wannan rikici ya biyo bayan sukar da Gwamna Abba ya yi wa Kwankwaso a karon farko tun bayan raba gari da suka yi a harkar siyasa a farkon wannan shekara.

Abba ya mayar da martani, inda ya ce shiru da yake yi ba tsoro ba ne.

Ya gargaɗi Kwankwaso da ya girmama kansa ya daina sukarsa , yana mai cewa idan ya ci gaba, zai bayyana wasu abubuwan da ba wanda zai ji daɗinsu.

Rikicin ya fara ne bayan da Gwamnan ya bar tafiyar siyasar Kwankwaso.

Daga baya Kwankwaso ya zarge shi da cin amanarsa, inda ya bayyana cewa gwamnan ya lashe zaɓe ne a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP kafin daga baya ya koma APC.

Tun daga lokacin, magoya bayan ɓangarorin biyu suka shiga takun saƙa da juna, musamman a kafafen sada zumunta, inda suke musayar zarge-zarge da kalaman cin zarafi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai